Advertisement
ZUMUNCI, ILIMI DA AMFANARWA!A yayin gudanar da shirin Sawa’idul Ika na Africa TV3 a Kaduna, malamai daga ƙasashen Najeriya, Ghana da Nijar sun samu damar haɗuwa, sada zumunta, musayar ilimi da gogewa, tare da ƙarfafa zumuncin ’yan’uwa.
Alhamdulillah! An amfana, an kuma amfanar. Haɗuwa irin wannan tana ƙara dankon zumunci, fahimtar juna da haɗin kai tsakanin malamai.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara ƙarfafa zumuncinmu, Ya sanya albarka a cikin wannan haɗuwa, sannan Ya saka wa jami’an Africa TV3 da alkhairi bisa wannan kyakkyawan shiri.
Allah Ya haɗa kanmu a kan alkhairi, Ya ƙara mana ilimi mai amfani da aiki na gari.
An amfana, an amfanar!
Advertisement
Event venue
Institution and Research, Abuja, Nigeria
Tickets