Advertisement
MURNAR CIKA SHEKARA TAKWAS DA FARAWA 8th ANNIVERSARY.Shekaru bakwai da suka wuce muka fara abu kamar wasa da yawa suna ganin inaa ai Nasmatu Muhammad ta yi yaranta da yawa ga wannan kasuwancin. Yanayin shi da zurfin ilimin da ake bukata gareshi duk ta yi kankanta. Na toshe kunnuwa na ga maganganun su da zan fara na ce Bismillahirrahmanirrahim. Na tsuduma da karfin hali. Da dan ilimi da sanin kayan da nake da shi kasancewar Sana'ar ta gida ce na saba ganin yadda ake yi sai na dora. Ni fa kawai na zamanantar da Sana'ar ne da na ce a Media zan yi tawa. Ai kuwa kamar wasa dama an ce kana iya samun kwarewa a kan abin da kake son yi sama ga abin da zaka karanta amma baka da sha'awa ta yin shi. Kasuwanci dai gashi nan Allah ya sa albarka. Daidai gwargwado cikin Nigeria babu jihar da ban taba aika kayana ba kudanci da arewacin ta. Haka ma wasu daga cikin kasashen wajen ta. Wannan abin farin ciki ne da ba zan iya misalta muku yadda ni nake jin shi ba. Ina yi wannan bayanin ne duka saboda yau nake cika shekaru 8 cif cif da fara wannan Sana'ar. Godiya da yabo sun tabbata ga Allah. In dai kin taba sayen magungunan Garkuwar Mata Nasmat kika ji dadin aikin su zo ki min bayani ta nan. Kuma ki yi ma cibiyar addu'a da murnar cika shekara takwas da kafuwa. Kamar kullum dai ni burina shi ne ko wace Matar aure ta yi farin ciki a gidan aurenta. ππ
Garkuwar Mata Nasmat taku ce. π
Advertisement
Event Venue & Nearby Stays
Iddo, Lagos, Nigeria
Concerts, fests, parties, meetups - all the happenings, one place.










