Kimtsa Ƴaƴa Mata Kafin Al'ada

Wed, 08 Apr, 2026 at 12:00 am UTC+01:00

Wuse II, Abuja | Abuja

Lambun Ma'aurata
Publisher/HostLambun Ma'aurata
Kimtsa \u01b3a\u01b4a Mata Kafin Al'ada Yanda za ki Shirya 'Yarki Don Fara Al'adarta Ta Farko 🌸
Balaga wani muhimmin lokaci ne kuma galibi mai rikitarwa ga 'yan mata. Ɗaya daga cikin manyan matakan da ake fuskanta shine fara al'ada (wato haila). A matsayinku na iyaye, kuna da mahimmiyar rawar da za ku taka wajen ganin wannan sauyi ya zo ma ƴaƴayrn ku a sauƙaƙe, ta hanyar ba su ilimi, da kuma ba su ƙarfin gwiwa. Tattaunawa a bayyane da tanadi na iya hana firgici da kuma tabbatar da cewa 'yarku jin cewa tana da wani kwarin gwiwa da kuma iya tafiyar da al'amuranta
Yaushe Ya Kamata a Fara Tattaunawar?
Lokaci mafi dacewa da za a iya yin magana game da al'ada shine kafin ta fara yi. Balaga na iya farawa ne tun daga shekara 8 ko 9, don haka fara waɗannan tattaunawar a wannan shekarun shawara ce mai kyau sosai. Aƙalla a fara nusasshe su cewa akwai wani abu na nan zuwa indai da rai, kuma iɗan sun fara tun da wurwuri ba za a samu wata matsala ba ɗomin tuni suna da masaniya kan abin ko da kuwa ƴar kaɗance masaniyar. Kada a jira wai har sai yarinya ta fara; hakan na iya zama abin tsoro. A riƙa sako batun a cikin hirarrakin yau da kullum game da lafiya da kuma girma. Abubuwan da Za a Tattauna: Muhimmai1.
Mece ce Al'ada?
A yi mata bayani kan mece ce al'ada cikin sauƙi da harshen da za ta iya ganewa. Al'ada wani tsari ne na halitta inda jiki ke zubar da bangon mahaifa, wanda ke cike da jini da wasu sassan jiki. Wannan alama ce da ke nuna cewa jikinta yana cikin koshin lafiya kuma yana girma yadda ya kamata. A nuna mata cewa cewa ba fa ciwo ba ne sai ma wata alama da ke nuna cewa ita ɗin mace ce lafiyayya.
A yi amfani da kalmomi masu sauƙi, da kwatanve da wani abu da zata gane. Kalmomin su kasance kuma ba waɗanda za su tsorata ta ba kamar: "Hanya ce da jiki ke amfani da ita wajen tsaftace kansa." Za a iya amfani da kwatance kamar kalanda: "Jikinta na shirya wani 'gida' ne ga jariri a kowane wata, idan kuma babu jaririn, sai jikin ya tsaftace gidan don shirin wani wata mai zuwa.
"2. Abubuwan da Za a Yi Tsammani:
Canje-canje na Jiki da na tunani: A yi mata bayani cewa al'ada ba wai zubar jini ba ne kawai. Tana iya fuskantar ciwon mara ko na baya, ciwon nono, kumburin ciki, gudawa, tashin zuciya da amai, ciwon kai, ko gajiya, ko kuma wasu alamun ma na daban. Domin kowane wata zai iya zuwa da wanis sabon salom da ba irin na watannin baya ba. Waɗannan duka alamomi ne na al'ada da ke nuna cewa al'adarta ta kusa zuwa.
Yawan Jini (Flow): A kwatanta mata yadda jinin zai kasance. Yana iya zama ruwan hoda-hoda ko ruwan ƙasa a farko, daga baya kuma ya koma ja wur. A yi mata bayani cewa jinin na iya zama kaɗan ko kuma mai yawa kuma zai iya bambanta a kowace rana.
Canje-canjen Tuanni da Motsin Rai: Canje-canjen da ake samu a sinadaran jiki (hormones) na iya haifar da sauyin yanayin motsin rai, saurin fushi, ko yawan baƙin ciki kafin ko kuma a lokacin da ake yin al'ada. A tabbatar mata cewa waɗannan abubuwan na al'ada ne kuma na ɗan wani lokaci ne kawai.
3. Yadda Za Ta Kula da Kanta:
Tsafta da Ingantattun Kayayyaki: Wannan wani muhimmin bangare ne na tattaunawar. A nuna mata nau'ukan kayayyakin al'ada da ake da su kuma a yi mata cikakken bayanin yadda ake amfani da su.
Audugar Mata (Pads): Waɗannan su ne aka fi amfani da su kuma suka fi sauƙin farawa da su. A yi mata cikakken bayanin yadda ake manna audugar a jikin ɗan kamfai da kuma lokacin da ya kamata a canza (kowane awa 3-4, ko kuma idan ya cika). A jaddada muhimmancin naɗe pads ɗin da aka yi amfani da shi a takarda ko leda kafin a jefa a kwandon shara. Kada a taɓa jefa audugar pad a cikin masai, domin tana toshe masai wanda hakan kan jawo babbar ɓarnar tsohewa sai an yi ta faman neman masu gyara.
Ƙunzugun Tampons: Wannan auduga ce mai kauri cukus ba kamar pad ba. A yi mata bayani cewa ana iya amfani da tampon nan gaba, amma don farkon al'adarta, pads ne suka fi dacewa. Idan tana da sha'awa, a nuna mata yadda ake amfani da shi. A jaddada cewa dole ne a canza tampon kowane awa 4-8 don hana kamuwa da ƙwayoyin cuta.
Wandon Al'ada (Menstrual Underwear): Wannan wani zaɓi ne mai kyau da ba ya bata jiki. A yi mata bayanin cewa waɗannan wandunan na musamman ne masu tsotse jini kuma ana iya sa su su kaɗai ba ma sai an saka pad ba, ko kuma a matsayin karin matakan kariya.
Tsafta: A jaddada muhimmancin yin wanka a kai a kai don jiki ya kasance cikin tsafta da annashuwa. A ba ta shawarar ta riƙa canza pads ko tampon akai-akai kuma ta wanke al'aurarta a hankali da ruwan mai ɗan dumi da sabulu mai laushi, marar ƙamshi.
Samar da Jakar Taimakon Gaggawa: A taimaka mata ta haɗa wata 'yar ƙaramar jaka da za ta iya ɓoyewa a cikin jakar makarantarta. Wannan zai ba ta damar jin cewa tana cikin shiri kuma tana da iko kan al'amuranta. Kayan jakar ya kamata su haɗa da:pads guɗa biyu zuwa uku (ko wasu kayayyakin da ta fi buƙata) Wata ƴar ƙaramar leda da za a iya rufe wa don zuba wanda aka yi amfani da shi. Wani ƙarin ɗan kamfai saboda sauyawa. Takardar Gogaggewa (wet wipes) ko ɗan ƙaramin man tsaftace hannu (hand sanitizer).
Abin Yi Idan ya Faru a Makaranta
A tabbatar mata cewa idan ma al'adarta ta fara a makaranta, ba laifi ba ne. A yi mata bayani cewa za ta iya zuwa wurin nes (nurse) na makaranta, wata malamar da ta amince da ita, ko kuma wata kawarta don neman pads. Wannan zai kawar da tsoron shiga wani yanayi ba tare da shiri ba.
Rawar da Iyaye Za Su Taka: Tabbatarwa da Taimako. Yadda kuka nuna damuwarku shi ne abu mafi mahimmanci. Nuna halin kulawa, kwanciyar hankali, da ƙarfafawa zai sa ta ji cewa tana cikin cikakken aminci kuma an fahimce ta yanda ya kamata.
A yi murna da shi: A gaya mata cewa jikinta yana yin aikin da ya kamata ne. Wannan alama ce ta cikakkiyar lafiya da kuma zama cikakkiyar 'ya mace.
Ki ba ta labarin kanki: A taƙaice kuma cikin farin ciki, ki ɗan ba ta labarin yadda kika yi al'adarki ta farko don ƙulla dangantaka da kuma nuna mata cewa ba ita kaɗai ba ce, kuma ba kanta farau ba.
Amsa dukkan tambayoyinta: A samar da yanayin da za ta iya yin kowace irin tambaya ba tare da jin kunya ko shayi ba.
Magance ciwo: Idan tana fama da ciwon mara, a ba ta shawarar hanyoyi masu sauƙi kamar wanka da ruwan dumi, amfani da robar ruwan zafi, ko motsa jiki a hankali. Haka kuma, za a iya ba ta magungunan kashe zugi (pain relief) da ake saya a kantin magani kamar ibuprofen idan likita ya amince.
Ta hanyar bin waɗannan matakan, za ku iya taimaka wa 'yarku ta fuskanci wannan sabon mataki na rayuwarta cikin kwarin gwiwa, ilimi, da kuma yarda da kai. Za ta san cewa al'adarta wani abu ne na al'ada kuma na halitta na zama cikakkiyar mace, kuma za ta san cewa kina tare da ita don tallafa mata a kowane mataki.
Shin yaya aka kare da ke a zuwan al'adarki ta farko? Ke ma kwarma ihun kika dinga yi irin na 'Mimi' kina cewa wayyo kin fara bilhaziya da atini ta gaba? Ko kuwa ki na ƴar masaniya ba ki samu wannna firgicin ba?
Domin sanin wacece Mimi a shirya domin fitowar littafin mu mai suna: ' Balagar Mimi' don sanin yanda aka yi amfani da ilimin wajen saƙa Hausa Novel kan dabarun nusar da yara maza da mata yanda jikinsu ya ke sauyawa yayin tashen balaga da kuma bayanan kula da killace mutuncin kai ta hanyar samun cikakken sex education a Hausance, kuma a al'adance.
Idan littafin ya fito za a saka tallansa anan domin masu buƙatar karantwa don kaeunansu da kuma yaransu.
#sexeducation #lambunmaaurata #viralreelschallenge2025viralreelschallengejaiviralreelschallengeviralreelschallenge
Lambun Ma'aurata
LIKE
COMMENT
SHARE

Event Venue

Wuse II, Abuja, Nigeria

Icon
Concerts, fests, parties, meetups - all the happenings, one place.

Ask AI if this event suits you:

More Events in Abuja

African Regional Tennis Coaches Conference
Sun, 12 Apr at 12:00 am African Regional Tennis Coaches Conference

Wuse II, Abuja

Match day what is your prediction
Tue, 14 Apr at 08:00 am Match day what is your prediction

area 11 garki abuja, Abuja, Nigeria

TRADE NIGERIA PORTAL
Mon, 20 Apr at 12:00 am TRADE NIGERIA PORTAL

Federal Capital Territory

TRADE NIGERIA PORTAL
Mon, 20 Apr at 09:00 am TRADE NIGERIA PORTAL

Federal Capital Territory

Commonwealth Nurses and Midwives Federation Conference
Tue, 21 Apr at 10:00 am Commonwealth Nurses and Midwives Federation Conference

Nicon Luxury Hotel, Abuja, Nigeria

Workerlink Business Summit 2026
Fri, 24 Apr at 10:00 am Workerlink Business Summit 2026

Abuja Continental Hotel

Abuja is Happening!

Never miss your favorite happenings again!

Explore Abuja Events